Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA : Uganda ta ce za ta karbi ‘yan gudun hijirar na Afghanistan 2000 bisa bukatar Amurka.
Minista a gwamnatin Uganda, Esther Anyakun, ya ce rukunin farko na ‘yan Afghanistan 500 zai sauka a filin jirgin saman Entebbe, kuma za’a musu gwajin cutar korona da zarar sun sauka sanna a killace su.
Gwamnatin Amurka ce za ta kula da dukkan yaunin kula da su inji ministan.
Idan dai hakan ta kasance Uganda za ta zama wata kasa a nahiyar Afrika ta farko da ta karbi ‘yan gudun hijiran Aghanistan tun bayan da ‘yan Taliban suka kwace mulkin kasar.
Uganda dai ita ce kasa ta uku a duniya wajen karbar ‘yan gudun hijira.
342/